Filipe Luis na daf da barin Chelsea

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Chelsea ba za ta dauko dan kwallo ba sai wani dan wasanta ya bar kulob din

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce Filipe Luis na daf da barin Chelsea, bayan da ya taka mata leda shekara daya.

Luis dan kwallon Brazil ya buga wa Chelsea wasanni 26 tun lokacin da ya koma Stamford Bridge daga Atletico Madrid kan kudi £15.8m.

Mourinho ya ce zai sayo mai tsaron baya ta bangaren hagu, domin zai sayar da Felipe Luis nan bada dadewa ba.

Kocin ya ce ba za su dauko karin dan kwallo ba har sai wanda suke da shi ya bar Stamford Bridge.

Ana rade-radin cewa Chelsea za ta dauko dan wasan Augsburg Abdul Baba Rahman ne domin maye gurbin Luis.