An dakatar da Frimpong buga wasanni 2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce a gasar Premier da akwai saukin kalamun wariya da batanci ga dan kwallo

Hukumar kwallon kafar Rasha ta dakatar da tsohon dan wasan Arsenal Emmanuel Frimpong daga buga wasanni biyu.

Frimpong mai wasa a Ufa ya ce wa hukumar abin ya wuce wasa, bayan data hukunta shi kan zargin anci zarafinsa a kwallo.

Dan wasan ya ce an yi ta kiransa da sunan biri, har zuwa lokacin da aka bashi jan kati kan maida martani a karawar da suka yi da Spartak Moscow.

Hukumar ta ce ba za ta hukunta Spartak ba, domin bata ga hujjar da aka ci zarafin dan kallon a wasan.

Frimpong dan kwallon Ghana mai shekaru 23 ya nemi afuwa kan laifin da ya aikata, kuma bai halarci zaman yanke masa hukuncin ba.

A bara dan kwallon Congo Christopher Samba mai taka leda a Dynamo Moscow shi ma sai da aka hukunta shi kan irin laifin da Frimpong ya aikata.