"Damar Balotelli a Liverpool na hannunsa"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rodgers ya ce Balotelli ne ya kamata ya mai do da karsashinsa a Anfield

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce Mario Balotelli ne ke da damar tashi tukuru domin ya ci gaba da murza leda a Anfield.

Balotelli dan kasar Italiya mai shekaru 24, ba ya cikin 'yan wasan da suke buga wa Liverpool wasannin atisaye a Amurka.

Rodgers ya kuma ce ba shi da tabbaci idan dan kwallon zai ci gaba da wasanni a Liverpool a bana.

Balotelli ya koma Liverpool murza leda daga AC Milan kan kudi £16m, kuma kwallaye hudu ya ci tun lokacin da ya koma Ingila.

Dan kwallon wanda ya buga wasanni Premier biyar bara ya zura kwallo daya ne tak a raga a gasar.

Tuni Liverpool din ta sayo 'yan kwallo shida da za su buga gasar wasannin da za a fafata a bana.