Wenger na fargabar lokacin yin ritaya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wenger ya kara daukar kofin FA a bana wanda ya lashe a bara

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce idan ya tuna da batun yin ritaya daga horas da tamaula ya kan ji tsoro.

Wenger dan kasar Faransa zai shiga shekara ta 20 da yake jagorantar Arsenal, kuma ya ce ba shi da niyyar bin sahun Sir Alex Ferguson wanda ya yi murabus daga horas da United.

Tshohon kociyan Monaco ya soma jagorantar Arsenal a shekarar 1996, a inda ya dauki League da FA a kakar farko da ya jagoranci kungiyar.

Sai dai kuma rabon da ya dauki kofin Premier tun a kakar wasan 2003-04.

Wenger ya fuskanci kalubale a bara, yayin da wasu magoya bayan Arsenal suka yi wa kocin ihu a tashar jirgin kasa, bayan ta shi daga karawar da Stoke City ta doke su a Premier.