Bayern Munich ta amince ta dauko Vidal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arturo ya taimaka wa Chile lashe Copa America a karon farko da ta yi

Bayern Munich ta amince da yarjejeniyar dauko dan wasan Juventus Arturo Vidal, kuma ta ce ba za ta sayar da Thomas Muller ba.

Shugaban Munich, Karl-Heinz Rummenigge, ya bayar da tabbacin cewar Manchester United tana zawarcin dan kwallon.

Rummenigge ya kara da cewar akwai 'yan wasan da ba su da farashi a Munich, domin sai idan ba sa cikin hayyacinsu ne za su sayar da Muller.

Vidal mai shekaru 28, ya amince da kunshin yarjejeniyar da Munich ta yi masa tayi, kafin ya saka hannu idan likitocin kungiyar sun kammala duba lafiyarsa a makwonnan.

Munich za ta sayo Vidal kan kudi fam £26m wanda yanzu haka yake yin hutu bayan da ya taimaka wa Chile lashe Copa America da ta yi a karon farko.

Tuni Bayern ta sayo Douglas Costa daga Shakhtar Donetsk da mai tsaron raga Sven Ulreich da kuma Joshua Kimmich dukkansu daga Stuttgart.