Mensah ya koma murza leda Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mensah zai fara wasa aro a kungiyar Getafe shekara daya

Dan kwallon tawagar Ghana, Bernard Mensah, ya saka hannu a kungiyar Atletico Madrid domin ya buga mata tamaula.

Atletico ce ta bayar da sanarwar a shafinta na Internet cewar Mensah ya kulla yarjejeniya mai tsawo da zai yi mata wasanni.

Mensah mai shekaru 20, ya koma Atletico ne daga Vitoria Guimaraes ta Potugal kan kwantiragin shekaru shida.

Sai dai kuma Atletico Madrid za ta bayar da shi aro ga makwabciyarta Getafe, a inda zai taka mata leda tsawon kakar wasa daya.

Mensah ya ci kwallaye biyar a wasanni 30 da ya buga wa Vitoria, ya kuma ci kwallo daya a karawar da ya fara yi wa Ghana wasa ranar 8 ga watan Yuni da Togo.