Ramos zai ci gaba da taka leda a Madrid

Image caption Ramos ya buga wa tawagar kwallon kafar Spaniya wasanni 128

Kocin Real Madrid, Rafael Benitez, ya kara jaddada cewar dan wasan da Manchester United ke zawarci Sergio Ramos zai ci gaba da murza leda a Santiago Bernabeu.

A watan jiya United ta taya Ramos mai shekaru 29 £28.6m, yayin da Madrid wacce ke fatan dauko mai tsaron raga David De Gea daga Old Trafford ta ki sallama shi.

An ruwaito cewar Ramos bai yi farin ciki da tayin albashin da Madrid ta yi masa ba kan batun tsawaita zamansa a kungiyar.

Ramos ya buga wa Madrid wasanni 445 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Sevilla a 2005.

Kuma dan kwallon yana daga cikin 'yan wasan Madrid da za su kara da Manchester United a wasan sada zumunta a Australia ranar Asabar.