Arsenal ta lashe kofin Emirates na bana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau hudu kenan Arsenal tana lashe kofin Emirates

Arsenal ta dauki kofin Emirates na bana, bayan da ta doke Wolfsburg da ci daya mai ban haushi a karawar da suka yi ranar Lahadi.

Bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne Theo Walcott ya ci wa Arsenal kwallo da ya ba ta damar lashe kofin Emirates kuma na biyu bayan kofin Barclays Asia da ta lashe.

Arsenal ta fara yin wasa tun a ranar Asabar a inda ta doke Lyon 6-0, sauran kungiyoyin da suka fafata a gasar sun hada da Villareal da kuma Wolfsburg.

Sabon mai tsaron raga da Arsenal ta sayo daga Chelsea shi ne ya taimaka mata lashe kofi na biyu, kuma shi ne wanda ya tsare raga a wasannin da ta yi a Asia.

Wannan shi ne karo na hudu da Arsenal ta dauki kofin Emirates da ake yi a filin wasanta da aka fara tun 2007.

Arsenal wacce ta dauki kofin FA a bara za ta fafata da Chelsea zakaran kofin Premier a Wembley ranar Lahadi, domin lashe Community Shield, kuma wasan bude gasar Premier bana.