Za'a duba lafiyar Jovetic a Inter Milan

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Jovetic ya yi fama da yin jinya a Manchester City

Inter Milan ta ce likitocinta za su duba lafiyar dan wasan Manchester City, Steven Jovetic, domin ya koma buga gasar Serie A.

Sai dai Inter ba ta fayyace idan Jovetic zai koma wasa Italiya dungurungum ko kuma aro zai murza mata leda ba.

Inter ta ce Jovetic zai ziyarci Italiya ranar Litinin sannan a duga lafiyarsa ranar Talata a wata sanarwa da ta fitar.

Jovetic ya koma City daga Fiorentina a 2013 kan kudi £22m, yayin da ya ci kwallaye 11 daga wasanni 43 da ya buga, ya kuma yi fama da jinyar rauni a Ettihad.