Newcastle ta amince ta dauki Mbemba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chancel Mbemba shi ne dan wasa na uku da Newcastle ta sayo a bana

Newcastle United ta amince ta dauko mai tsaron bayan Anderlecht, Chancel Mbemba, da zarar ya samu takardun izinin buga tamaula a Ingila.

Mbemba mai shekaru 20 dan kwallon Jamhuriyar Congo ya amince da albashin da aka yi masa tayi, kuma tuni likitocin Newcastle suka kammala duba lafiyar dan wasan.

Dan kwallon ya buga wasanni 28 a Anderlecht wacce ta kammala a mataki na uku a kan teburin gasar Belgium a bara.

Mbemba ne dan wasa na uku da Newcastle United ta sayo a bana da suka hada da mai buga wasan tsakiya Georginio Wijnaldum da kuma mai zura kwallo a raga Aleksandar Mitrovic.