Angel Di Maria na daf da komawa PSG

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Angel Di Maria ya koma United daga Real Madrid a bara kan kudi £59.7m

Angel Di Maria na daf da komawa Paris St-Germain daga Manchester United kamar yadda dan wasan ya nemi izinin barin Old Trafford in ji Laurent Blanc.

Di Maria dan kwallon Argentina bai halarci sansanin atisayen da United ke yi a Amurka ba, kuma koci Louis van Gaal ya ce bai san dalili ba.

Blanc ya ce akwai damar Di Maria zai iya komawa PSG da taka leda, amma dai ba'a cimma kulla wata yarjejeniya ba.

Jaridar Faransa mai suna L'Equipe ta ruwaito cewar United ta amince ta sayar wa da PSG angel Di Maria kan kudi £46.5m.

A ranar Juma'a Van Gaal ya sanar da cewar Di Maria zai halarci wurin da United ke yin atisaye a Amurka, duk da rade-radin da ake cewar zai koma Faransa da murza leda.