Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Sojan Kyallu daga Arewa da Bahagon Mai Maciji daga Kudu

Da sanyin safiyar Lahadi aka ci gaba da wasannin damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali Zuma dake Dakwa a Abuja.

An fara ne da wasa tsakanin Shagon Bahagon Musa daga Arewa da Autan Faya daga Kudu, kuma turmi uku suka fafata babu kisa aka raba wasan.

Dambe tsakanin Shago na Kada Mutsa daga Arewa da Matawallen kwarkwada ya kayatar, sai dai shi ma wasan ba'a yi kisa ba.

Fafafawa tsakanin Shagon Bahagon Musa daga Arewa da Shagon Bahagon Sarka daga Kudu sun yi gumurzu kuma an biya 'yan kallo, sai dai shi ma wasan ba a yi kisa ba.

Daga karshen wasa an saka zare ne tsakanin Sojan Kyallu daga Arewa da Bahagon Mai Maciji, sun dambata matuka har tsawon turmi uku sarkin gida na Jafaru Kura ya raba karawar.