Manchester United ta dauko Romero

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Romero ne ya kamawa Argentina a gasar cin kofin duniya a Brazil

Manchester United ta dauko golan kasar Argentina Sergio Romero a yayinda ake ci gaba da fuskantar rashin tabbas a kan David De Gea.

Romero wanda tsohon golan Sampdoria ne, ya maye gurbin Victor Valdes, wanda Louis Van Gaal ya ce masa zai iya barin kulob din.

Romero, ya sanya hannu a kwangilar shekaru uku tare da United kuma ya taba aiki a karkashin Van Gaal a kungiyar AZ Alkmaar ta Netherlands.

"Dole ne mu shiryawa kakar wasa mai zuwa saboda barazanar da muke fuskanta daga Real Madrid a kan David De Gea," in ji Van Gaal.

Idan har De Gea ya ci gaba da zama a United, to zai yi goggaya da Ramero mai shekaru 28.