Stoke City ta dauko Ibrahim Afellay

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stoke City ta kammala a mataki na tara a kan teburin Premier bara

Dan wasan tawagar kwallon kafar Netherlands, Ibrahim Afellay, ya zama dan kwallon Barcelona na hudu da zai murza leda a Stoke City.

Afellay mai shekaru 29, ya rattaba hannu a Stoke bayan da kwantiraginsa ta kare da Barcelona wacce ya yi shekaru hudu da rabi a Nou Camp.

Dan kwallon ya yi wasanni tara a Barcelona, yayin da ya buga wasannin kakar bara aro a Olympiakos da kuma takaitatcen zama da ya yi a Schalke ta Jamus.

Kociyan Stoke Mark Hughes ya kuma tabbatar da cewar yana zawarcin dan wasan Ukraine Andriy Yarmalenko.

Kuma tuni Stoke City ta sayar da 'yan wasanta biyu kan kudi £15m jumulla da suka hada da Steven N'Zonzi da kuma Asmir Begovic.