Zan bar aiki saboda matata — van Gaal

Hakkin mallakar hoto
Image caption Van Gaal ya ce yana so ya samu lokacin da zai kula da iyalinsa.

Kociyan Manchester United Louis van Gaal ya ce yiwuwa ba zai sabunta kwantaraginsa da kolob din ba idan ya kare ba saboda alkawarin da ya yi wa matarsa cewa zai rika kula da ita sosai.

Van Gaal ya sanya hannu a kwantaragin shekaru uku da United, don haka kwantaragin zai kare a shekarar 2017.

Da aka tambaya shi, shin zai tsawaita kwantaraginsa a Old Trafford, Van Gaal ya shaida wa BBC Sport cewa zai "ajiye aiki" a karshen kwantaraginsa a shekarar 2017.

Ya ce, "Na yi wa matata alkawari. Yanzu haka mun kwashe shekaru da dama ba ma haduwa sosai. Don haka wannan shi ne dalilin da ya sa nake son kasancewa tare da ita."

Kociyan, mai shekaru 63 a duniya, ya kara da cewa "Na cimma burin da nake so na cimma na kasancewa kociya."

Da aka kara tambayar sa, shin akwai yiwuwar tsawaita kwantaraginsa, Van Gaal ya ce ba zai iya amsa tambayar ba saboda matarsa, Truus, "ba za ta taba lamincewa ba".

Ya ce "lokacin da muka hadu, lokacin dangantakarmu tana tafiya yadda muke so, na gaya mata cewa idan na kai shekaru 55 zan yi ritaya. A makon gobe zan cika shekaru na 64, kuma har yanzu ina aiki."