Algeria ta soke dauko 'yan wasa daga waje

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumar Algeria ta hana dauko 'yan wasa daga wajen kasar

Hukumar kwallon kafar Algeria ta soke dauko 'yan wasan tamaula daga wajen kasar nan take.

Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda matsalolin kudi da kasa samun kudaden waje domin biyan 'yan wasa da kudin diyya da sauran hakkin 'yan kwallo.

Haka kuma hukumar ta ce yanke wannan hukuncin zai ba ta damar yakar munanan dabi'un eja da suke kula da harkokin wasannin dan kwallo da suke jefa hukumar cikin rikici.

An amince da 'yan wasan da aka sayo daga waje da yanzu ke buga gasar Algeria da su ci gaba da murza leda har zuwa karshen kwantiragin da suka kulla da kungiyoyinsu.