Arturo Vidal ya koma Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Vidal shi ne dan kwallo na hudu da Bayern ta sayo a bana

Dan kwallon Chile mai taka leda a Juventus Arturo Vidal ya kammala komawa Bayern Munich domin ci gaba da murza leda.

Vidal mai shekaru 28, ya taimaka wa Juve lashe kofunan Seria A hudu, tun lokacin da ya koma kulob din daga Bayern Leverkusen a 2011.

Dan wasan wanda yana daga cikin tawagar 'yan kwallon Chile da ta lashe Copa America, ya saka hannu kan kwantiragin shekaru hudu a Munich.

Tuni dai Bayern ta sayo 'yan wasa da suka hada da mai wasan tsakiya Douglas Costa daga Shakhtar Donetsk da Joshua Kimmich daga Stuttgart da kuma mai tsaron raga Sven Ulreich.