Felipe Luis ya sake komawa Atletico

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A bara ne Chelsea ta sayo Luis daga Atletico Madrid

Dan kwallon Chelsea Felipe Luis ya sake komawa Atletico Madrid, bayan shekara daya da ya je Stamford Bridge.

Luis mai shekaru 29, dan wasan Brazil ya buga wa Chelsea wasanni 26, a inda ya lashe kofin Premier da League Cup a bara.

Dan wasan ya saka hannu a kwantiragin shekaru hudu domin ya ci gaba da murza leda a Atletico ta Spaniya.

Chelsea ta sayo Felipe Luis daga Atletico Madrid kan kudi £15.8m a bara.

Ana rade-radin cewar Mourinho zai dauko dan kwallon tawagar Ghana mai murza leda a Augsburg Abdul Baba Rahman domin ya maye gurbin Luis.

Haka kuma Atletico ta sake bayar da Javier Manquillo wanda ya yi wasa aro da Liverpool zuwa Marseille ta Faransa.