Platini zai tsaya takarar shugabancin Fifa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Platini da Blatter a yanzu ba sa ga maciji

Shugaban Uefa Michel Platini a cikin wannan makon ake saran zai sanar da cewa zai tsaya takarar shugabancin Fifa.

BBC ta fahimci cewa Platini bayan samun goyon bayan hukumomin kwallon kafa da dama a duniya zai nemi takara a zaben da za a gudanar a ranar 26 ga watan Fabarairu.

Dan shekaru 60, Platini wanda dan kasar Faransa ne watakila a ranar Laraba ya bayyana aniyarsa.

Sepp Blatter mai shekaru 79 shi ke jagorantar Fifa tun daga shekarar 1998.

Blatter ya fuskanci matsin lamba saboda batun cin hanci da rashawa a Fifa abin da ya talista masa cewa zai sauka daga kujerar.