Marseille ta dauki Abou Diaby

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Diaby ya buga wa Arsenal wasanni 182 tun daga 2006

Tsohon dan kwallon Arsenal Abou Diaby ya saka hannu a Marseille domin ya buga mata tamaula, bayan da ya ki amince wa da tayin da West Brom ta yi masa.

Diaby mai shekaru 29, ya ziyarci West Brom a makon jiya har ma likitocin kulob din sun duba lafiyarsa, amma daga baya ya zabi taka leda a Faransa maimakon a Ingila.

Dan wasan ya koma murza leda a Faransa shekaru tara, bayan ya bar kungiyar Auxerre.

Arsenal ce ta amince da dan wasan ya bar Emirates, bayan wasanni 182 da ya yi wasa a Emirates din tun daga 2006.

Marseille ta kuma sayo tsohon dan wasan Arsenal, mai buga wasan tsakiya Lassana Diarra a makon jiya.