"Platini ba zai iya kawo sauyi a Fifa ba"

Image caption Bility shi ne dan Afirka na biyu bayan Hayatou da ya nemi takarar kujerar Fifa

Shugaban hukumar kwallon kafar Liberia, Musa Bility, ya ce ba za a amince da takarar Michel Platini ta neman shugabancin Fifa ba.

Platini ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin hukumar kwallon kafar ta duniya wato Fifa a ranar Laraba.

Bility ya shaida wa BBC cewar "Duniya ce ta bukaci a kawo sauyi kan harkokin tamaula da kuma sauya wadanda ke jagorantar wasan".

"Platini ba zai iya wakiltar sauyi ba, tunda ya yi mataimakin Fifa shekaru takwas, bai kamata ya maye gurbin Blatter ba, abin da ba za a amince da shi ba ne".

Bility da Platini da kuma Zico ne suka nuna sha'awar yin takarar shugabancin Fifa a zaben da za a yi ranar 26 ga watan Fabrairu, domin maye gurbin Sepp Blatter.

An zargi hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa da cin hanci da rashawa da ya yi sanadiyyar damke wasu daga cikin jami'anta.