Chung na son maye gurbin Sepp Blatter

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yerima Ali na Jordan ne ya maye gurbin Chung a matsayin mataimakin shugaban Fifa

Chung Mong-joon na Korea ta Kudu ya ce yana son ya maye gurbin Sepp Blatter a matsayin shugaban Fifa na gaba.

Chung ya taba yin mataimakin shugaban Fifa, kuma shi ne wanda ya fi yawan hannun jari a babbar masana'antar Hyundai..

Ya kuma shaida wa BBC cewar Platini ba shi ne mutumin da ya da ce ya shugabanci Fifa ba.

Ya kuma ce idan aka zabe shi ba zai ce zai mori alfarmar da ke aikin ba, zai mai da hankali ne kawai wajen sauya alkiblar hukumar da yadda ake gudanar da ita.

Chung mai shekaru 63, yana da jarin £769m in ji mujallar nan ta Forbes.

A ranar Laraba ne Platini ya sanar da aniyar zai yi takarar shugabancin Fifa a zaben da za a yi a watan Fabrairun badi.

Sepp Blatter wanda ya fara shugabantar Fifa tun 1998 ya ce zai yi murabus, bisa zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye hukumar.