"Muna fuskantar matsala kan De Gea"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption PSG ta doke United 2-0 a International Champions a Chicago ranar Laraba

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce suna fuskantar matsala kan batun sayar da David De Gea.

De Gea mai shekaru 24, mai tsaron ragar, na son ya koma Real Madrid taka leda, amma United ta bukaci sai in za a sayar mata da Sergio Ramos.

Shi kuwa kociyan Real Madrid, Rafael Benitez ya ce dan wasan mai tsaron baya zai ci gaba da buga tamaula a Bernabeu.

Van Gaal ya shaida wa BBC cewar "Muna da matsala da ke bai wa De Gea takaici da mu kanmu da kuma kungiyar, domin golan yana son komawa Madrid da murza leda.

United ta sauya De Gea bayan da aka dawo daga hutu a karawar da Paris St-Germain ta doke United 2-0 ranar Laraba a wasannin International Champions Cup a Chicago.