Chelsea ce kan gaba a Ingila– Shearer

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tawagar Chelsea bayan ta yi zarra a Ingila

Zakarar kwallon Premier na Ingila, Chelsea ce kungiyar da ta fi kowacce karfi a wannan kakar wasan da za a soma, in ji tsohon kyaftin din Ingila Alan Shearer.

Chelsea ce ta lashe kofin a kakar wasan da ta wuce inda ta bai wa Manchester City tazarar maki takwas.

"Chelsea ta yi zarra a kakar wasan da ta wuce, kuma tabbas daga watan Fabarairu gasar za ta yi zafi," in ji Shearer.

Tsohon dan wasan Newcastle din ya ce Manchester United na da jan aiki a gabanta, a yayinda kocin Liverpool Brendan Rodgers ke cikin matsin lamba.

A cewar Shearer kungiyoyin Watford da Bournemouth da kuma Norwich za su iya fuskantar koma baya a gasar.