Aubameyang ya sabunta kwantaragi a Dortmund

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pierre-Emerick Aubameyang ya haskaka a gasar Bundesliga

Dan kwallon Borussia Dortmund, Pierre-Emerick Aubameyang ya sabunta kwantaraginsa domin ci gaba da taka leda a kungiyar har zuwa kakar wasa ta 2019-2020.

Aubameyang mai shekaru 26 ana ta alakantashi da wasu manyan kungiyoyi a Turai ciki hadda Arsenal.

Dan wasan Gabon din ya hade ne da Borussia daga kungiyar St Etienne inda a kakar wasan da ta wuce ya zura kwallaye 16 cikin wasanni 33 a gasar Bundesliga.

"Zuciyata ba ta son na bar wannan kulob din kuma bana son mu rabu," in ji Aubameyang.