A Beijing za a yi gasar Olympics ta 2022

Image caption Beijing zai kasance birni na farko da ya karbi bakuncin gasar Olympics ta bazara da ta hunturu.

An zabi birnin Beijing na kasar China domin ya karbi bakuncin gasar Olympics ta lokacin hunturu wadda za a yi a shekarar 2022.

Birnin zai kasance na farko da ya karbi bakuncin gasar Olympics ta lokacin bazara da kuma ta lokacin hunturu.

Birnin Almaty na Kazakhstan ne ya sha kaye a hannun Beinjing a fafatawar da suka yi ta kut-da-kut kan karbar bakuncin gasar.

Da ma dai an yi tsammanin birnin Beijing ne zai karbi bakuncin gasar za su zaba a taron da suka yi a Kuala Lumpur.

Mahukunta a birnin na Beijing sun ce nasarar da suka yi ta karbar bakuncin gasar Olympics shekaru bakwai da suka wuce ita ce za ta ba su damar sake karbar bakuncin gasar.