Troost-Ekong ya koma kulob din Gent

Image caption William Troost-Ekong ya shiga yarjejeniya da Gents.

Dan Najeriya mai tsaron gida, William Troost-Ekong zai koma kulob din Gent ta kasar Belgium.

Matashin mai shekaru 21, wanda a da yake tare da Tottenham ya baro kulob din Groningen na Holland inda ya shiga sabuwar yarjejeniya ta shekaru uku.

Za'a dai ba da aron sa na wa'adin shekara guda a kulob FK Haugesund na Norway.

"Na yi farin cikin wannan yarjejeniya da zakarun Belgium, kuma na dauki lokaci ina tunani a kan matakin da zan dauka," in ji Troost-Ekong.

Dan wasan na Super Eagles ya ki amincewa da tayin kudin da kulob din Rostov na Russia ya yi masa, kuma har ma da zawarcin da kulob din SD Ponferradina na Spaniya da kuma wasu cikin zakarun Turai suka yi masa.