United ta gabatar da kayan wasanninta

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ranar Asabar za a fara gasar Premier bana

Manchester United ta gabatar da sabbin kayan wasan da za ta yi amfani da su a gasar wasannin bana da Adidas ta samar mata.

Kamfanin Adidas ne ya kulla yarjejeniya kudi £75m da United kan zai dunga yi masa tallan kayayyakin wasannisa.

United ce ta sanar da saka hannu a kwantiragi da Adidas na tsawon shekaru 10 a Yulin 2014, amma ba ta gabatar da kayan ba, bisa karasa kwangila da Nike tsawon shekaru 13 da suka cimma.

Wannan shi ne karon farko da Adidas ya yi wa United kayayyakin wasanni a shekaru 24, har ma kulob din ya ce "Zanen da aka yi wa kayan sun kayatar".

Chelsea da Liverpool suna daga cikin kungiyoyin da suma za su bayyana sabbin kayan wasan su.

United za ta fara gasar Premier bana a Old Trafford da Tottenham ranar 8 ga watan Agusta, sannan za ta dawo gasar cin kofin zakarun Turai.