Za'a duba lafiyar Di Maria a PSG

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Angel Di Maria ya wakilci Argentina a gasar Copa America da Chile ta lashe

Likitocin Paris St-Germain na daf da duba lafiyar dan kwallon Manchester United, Angel Di Maria, domin ya koma Faransa da taka leda.

Di Maria wanda United ta sayo daga Real Madrid a bara kan kudi £59.7m, zai ziyarci Doha ranar Lahadi domin tattaunawa da jami'an PSG.

Ana hasashen cewa PSG za ta sayi dan kwallon Argentina da zai kai kudi £44.5m.

Tun bayan da aka kammala gasar Copa America a Chile, Di Maria bai halarci atisayen da United ta yi a Amurka ba.

Di Maria ya koma Old Trafford a Agustan bara, bayan da ya taimaka wa Madrid lashe kofin zakarun Turai na goma da ta dauka a 2014.