Sakamakon wasannin Damben gargajiya

Image caption Damben Sarka da Garkuwan Cindo ba'a yi kisa a wasan ba

A ci gaba da wasan Damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali Zuma dake Dakwa a Abuja Nigeria an fafata a wasannin safe a ranar Lahadi.

An fara karawa ne tsakanin Dogon Bahagon Dan sanda daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa, kuma a turmi na biyu Dogon Bahagon Dan Sanda ya yi kisa.

Dambe tsakanin Shago na Kada Mutsa daga Arewa da Autan Faya daga Kudu ya kayatar, sai dai turmi biyu suka yi, kuma babu kisa Sarkin Gida na Jafaru Kura ya raba wasan.

A wasan da aka saka zare tsakanin Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu da Shagon Musan Kaduna daga Arewa bai dauki lokaci ba, domin nan take Shagon Musan Kaduna ya kashe garkuwan Shagon Alabo a turmin farko.

An kuma yi damben manya tsakanin Garkuwan Cindo daga Arewa da Sarka daga Kudu na turmi biyu, sai dai kuma ba'a yi kisa a fafatawar ba.