Ronaldo ya yi wa Mendes kyautar girma

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Mendes ya dade yana kula da harkokin wasannin Ronaldo

Dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya yi wa mai kula da harkokin wasanninsa Jorge Mendes kyautar tsibiri a Girka bisa taya shi murnar aure da ya yi.

Ba a bayyana sunan tsibirin da Ronaldo ya kyautar ba, amma rahotanni na cewa wurin yana da tsadar gaske da aka gina kan miliyoyi da dama.

Mundo Deportivo ta rubuta a shafinta na Internet cewar Ronaldo ya san tsibirin Girka ciki da waje domin wajen da yake yin hutunsa ne

A ranar Lahadi Mr Mendes ya auri Sandra a Portugal, kuma Sir Alex Ferguson yana daga cikin manyan baki da suka halarci bikin.

Bayan da fitattun 'yan wasa daga Spaniya da Portugal da sauran kasashe da suka halarci taron, shi ma shugaban Madrid Florentino Perez da na Benfica Luis Filipe Vieira da kuma na Chelsea Roman Abramovich sun halarci bikin.

A cewar labaran ABC, Mr Mendes daya ne daga cikin masu arziki a Portugal, a inda ta ce yana da jarin da ya kai €100m.