"Babu inda Bale da Benzema za su koma"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Benitez ya ce 'yan wasan biyu suna da rawar da suke takawa a Madrid

Kocin Real Madrid, Rafael Benitez ya ce baya tsammanin Gareth Bale da Karim Benzema za su bar kulob din.

Ana rade-radin cewar Manchester United na zaracin Bale mai shekaru 26, yayin da ake danganta dan wasan Faransa Benzema da komawa Arsenal.

Kocin ya yi wannan kalamin ne a gaban 'yan jaridu kan wasan sada zumunta da za su yi da Tottenham ranar Talata kafin su fafata da AC Milan da kuma Bayern Munich mai masaukin baki.

Benitez ya ce Gareth dan wasa ne mai mahimmaci a Bernabeu, kuma Benzema ba zai koma wata kungiyar da murza leda ba.

Rashin tabbas din Bale a Madrid ya karo taso wa ne bisa dan kwallon United Angel Di Maria dake daf da komawa Paris St-Germain.