An kashe £500m kan sayo 'yan wasa a Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sterling shi ne dan wasan da aka sayo da tsada a Premier a bana

I zuwa yanzu an kashe £500m kan sayo 'yan wasan tamaula a Premier kasa da £335m da aka kashe a bara, duk da saura makwonni hudu a rufe kasuwar sayen 'yan kwallon.

Raheem Sterling wanda Manchester City ta saya kan kudi £44m, shi ne wanda aka saya mafi tsada a gasar ta Premier a bana.

Wani masani kan cinikayya Rob Wilson ya ce za a iya kashe kudade masu yawa wajen dauko 'yan kwallo ganin karin kudin shiga da kungiyoyin za su samu kan nuna wasanninsu a talabijin.

Za a rufe kasuwar sayen 'yan kwallon kafar Turai a Ingila ranar Talata 1 ga watan Satumba.

Haka kuma daga tsakanin kakar wasan 2016-17 za a kara ladan nuna wasan Premier a talabijin daga £3.018bn zuwa £5.136bn tsawon shekaru uku.

Duk kulob din da ya lashe kofin Premier bana zai karbi kudi £150m, yayin da kungiyoyin da suka yi na karshe a gasar kowacce za a ba ta £99m.