Real Madrid ta doke Tottenham 2-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bale na fama da kalubale a murza leda da yake yi a Madrid

Gareth Bale ya ci tsohuwar kungiyarsa Tottenham a karawar da Real Madrid ta samu nasara da ci 2-0 a wasan sada zumunta a Audi Cup a Jamus.

Wannan ne kuma karon farko da Bale ya fuskanci Tottenham a wasa, tun bayan da Madrid ta saye shi daga kungiyar kan kudi £85.3m.

James Rodriguez ne ya fara ci wa Madrid kwallo a fafatawar da suka yi ranar Talata a filin wasan Bayern Munich, Allianz Arena.

Wasannin atisayen tunkarar kalubalen bana da ake yi a Jamus domin lashe Audi Cup ya kunshi mai masaukin baki Bayern Munich da AC Milan da kuma Tottenham din.