Ferdinand: Ya kamata Stones ya koma United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Stones ya koma Everton da murza leda a 2013

Rio Ferdinand ya ce ya kamata mai tsaron bayan Everton, John Stones ya koma taka leda Manchester United ba Chelsea ba.

Everton ta ki amincewa da tayin £20m da Chelsea ta yi wa Stones dan kwallon Ingila, wanda ake cewa United ma na sha'awar sayo shi.

Tsohon dan wasan United Ferdinand ya ce da zarar ya koma Chelsea da taka leda ba za a dunga saka shi a wasa a kai a kai ba.

Stones wanda ya koma Everton daga Barnsley a 2013, ya buga wasanni 44 a gasar Premier.

Kocin Everton, Roberto Martinez ya ce yana son Stones ya ci gaba da wasa a kulob din domin yana da rawar da yake takawa.

United tana da masu tsaron baya da suka hada da Chris Smalling da Phil Jones da Marcos Rojo da Jonny Evans da Paddy McNair da Tyler Blackett da kuma Daley Blind.