Oliseh ya kagara ya nuna kwarewarsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oliseh ya buga wa Super Eagles wasanni daga 1993 zuwa 2002

Sabon kocin Nigeria, Sunday Oliseh ya ce a shirye yake ya kalubalanci masu cewar ba shi da kwarewar da ta kamata ya horas da Super Eagles.

Oliseh mai shekaru 40, tsohon dan kwallon Borussia Dortmund da Juventus ya saka hannu kan kwantiragin shekaru uku da NFF domin ya yi kocin tawagar kwallon kafar Nigeria.

Hakan ne kuma ya sa ya maye gurbin Stephen Keshi, wanda aka kora a farkon watan Yuli, bisa samunsa da laifin neman aikin horas da Ivory Coast, bayan yana da kwantiragi da NFF.

Oliseh ya horas da kungiyar Vervietois mai buga karamar gasar Belgium daga tsakanin 2008 zuwa 2009, tun daga lokacin ya zama mamba a kwamitin tsare-tsare na Fifa da zama mai sharhin wasanni kuma jami'in da ake tuntuba kan harkar tamaula.

Kocin ya yi shagube cewa "Ko da akwai wani tsohon dan wasan Afirka wanda ya taba horas da babban kulob a Turai?