"Arsenal za ta lashe kofuna a bana"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ta dauki Community Shield bayan da ta doke Chelsea

Dan wasa daya ne ya rage wa Arsenal ta sayo ta iya cin kofunan Turai in ji Alisher Usmanov daya daga cikin mafiya yawan hannun jari a kulob din.

Mai tsaron raga Petr Cech ne kadai Arsene Wenger ya sayo zuwa Arsenal daga Chelsea a bana.

Kuma ana rade-radin cewar Karim Benzema na Real Madrid zai koma Arsenal kafin wasan Premier da za ta fara da West Ham ranar Lahadi.

A wata hira da CNN Usmanov, ya ce "In ban da wurin dan wasa daya, ina ganin Arsenal ta shirya cin kofunan Turai".

A ranar Lahadi Arsenal ta doke Chelsea a wasan Community Shield da ci daya mai ban haushi, kuma Alex Oxlade-Chamberlain ne ya ci kwallon.

Chelsea ake hasashen za ta kara lashe Premier bana, amma kuma Arsenal wacce ta kammala gasar bara a mataki na uku za ta kalubalanci daukar kofin.