Crystal Palace ta dauki Bakary Sako

Hakkin mallakar hoto crystalpalacetwitter
Image caption Sako shi ne dan wasa na biyar da Palace ta dauka a bana

Kungiyar Crystal Palace ta kammala daukar dan kwallon tawagar Mali Bakary Sako kan yarjejeniyar shekaru uku.

Sako mai shekaru 27 zai koma Palace ne da murza leda, bayan da kwantiragin da ya kulla da Wolves mai buga gasar Championshin ta kare.

Sako ya ci wa Wolves kwallaye 36 daga wasanni 118 tun lokacin da ya koma kulob din daga St Etienne a 2012.

Haka kuma kocin Palace, Alan Pardew ya musanta cewar suna zawarcin kyaftin din Newcastle United Fabricio Coloccini.

Sako shi ne dan kwallo na biyar da Palace ta sayo a bana, bayan Yohan Cabaye da Alex McCarthy da Patrick Bamford da kuma Connor Wickham.