Na ji dadin komawa PSG - Di Maria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Di Maria bai haskaka ba a United

Angel Di Maria ya ce "ya ji dadin" koma wa Paris St-Germain daga Manchester United, shekara guda bayan ya bar Real Madrid.

Dan kwallon Argentina mai shekaru 27, an gwada lafiyarsa a Qatar a yayinda zai kamalla komawa PSG a kan fan miliyan 44.

Di Maria ya shaida wa beIN Sports cewar "Na yi matukar jin dadin koma wa Paris St-Germain. Kungiyar na da mahimmanci sosai."

Kawo yanzu PSG da United ba su ce komai ba game da yarjejeniyar.

Di Maria ya zura kwallaye hudu cikin wasanni 32 a United tun bayan da ya bar Real Madrid a watan Agustan bara.