Mayweather zai kara da Berto a Satumba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Floyd Mayweather ya lashe wasanni 48 da ya dambata

Floyd Mayweather zai fuskanci Andre Berto ranar 12 ga watan Satumba, kuma zai iya kafa tarihin yawan lashe wasanni 49 da Rocky Marciano ya yi a baya.

Berto tsohon zakaran kambun ajin welterweight ya lashe wasanni 30, sanan aka buge shi wasanni uku kafin karawar da zai yi da Mayweather.

Dan damben Burtaniya Amir Khan ne ya yi fatan zai fuskanci Mayweather, bayan da ya dambace Chris Algieri a watan Yuni.

Idan Mayweather ya lashe wasan zai yi kan-kan-kan da Marciano wanda ya yi nasara a wasanni 49, sannan ba a doke shi ba tun lokacin da ya zama kwararren dan dambe.

Haka kuma a baya Mayweather ya ce idan ya kara a wasa na 49 zai yi ritaya daga yin damben boksin.