Everton na bukatar 'yan wasa uku — Martinez

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Martinez ya ce ba za su fuskanci matsala ba.

Kociyan Everton Roberto Martinez ya ce yana bukatar sayen karin 'yan wasa uku kafin a rufe kasuwar sayen 'yan wasa ranar daya ga watan Satumba.

Kulob din zai fara karawar Premier a gida da sabbin 'yan wasa uku kawai da ya saya da kungiyar Watford wadda ta yi nasarar shigowa gasar a bana.

Martinez ya ce: "ba za mu taba kawo dan wasa domin kawai ya zama cikon-benci ba."

A bana dai, kulob din Everton ya sayi 'yan wasan gaba, Gerard Deulofeu da David Henen da kuma dan wasan baya Tom Cleverley.

Martinez ya kara da cewa, "ina tsammani ba za mu fuskanci wata matsala ba idan aka rufe kasuwar sayen 'yan wasa. Za mu tabbatar mun samu 'yan wasa masu inganci."