West Ham ta doke Arsenal 2-0 a Emirates

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasanni 10 baya da suka yi Arsenal ce ta samu nasara

Sabon kocin West Ham Slaven Bilic ya fara gasar Premier da kafar dama, bayan da ya jagoranci kulob din doke Arsenal 2-0 a gasar Premier ranar Lahadi.

Arsenal wacce ke masaukin baki an fara zura mata kwallo ne a raga ta hannun Cheikhou Kouyate da ka, bayan da ya samu kwallo daga bugun tazara.

Bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne daga yadi na 20 Mauro Zarate ya kara cin Arsenal ta biyu, yayin da 'yan bayan Arsenal suka yi kuskure.

Arsenal ce ta mamaye karawar da suka yi, sannan ta samu dama tun kafin a tafi hutu a inda Aaron Ramsey ya buga kwallo kuma ta bugi turke.