Swansea ta samu maki a Chelsea karo na farko

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A karon farko Swansea ta samu maki daya a Stamford Bridge

A karon farko Swansea ta samu maki a Stamford Bridge, bayan da ta buga 2-2 da Chelsea a gasar Premier bana da aka bude.

Chelsea ce ta fara cin kwallo ta hannun Oscar, sai dai kuma Andew Ayew ya farke wa Swansea kwallon da aka zura mata.

Chelsea ta kara ta biyu bayan da dan wasan Swansea Fernandez ya ci gida saura minti 15 a ta fi hutun rabin lokaci.

Swansea ta farke kwallo ta biyu ta hannun Gomis daga bugun fenarity, bayan da Courtois ya yi masa keta

Haka kuma Chelsea ta karasa fafatawar da 'yan wasa 10 a fili, bayan da aka bai wa Courtois zan kati