Leicester ta fara tauna tsakuwa a Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sabon koci Claudio Ranieri ya shirya buga Premier bana

Leicester City ta fara tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro a inda ta lallasa Sunderland da ci 4-2 a gasar Premier bana da suka fafata a ranar Asabar.

Leicester ta zura kwallaye uku a minti 30 din farko da fara tamaula, kuma Jamie Vardy ne ya fara cin ta farko da ka.

Riyad Mahrez ne ya ci ta biyu da kuma ta uku daga bugun fenariti, bayan da Lee Cattermole na Sunderland ya yi masa keta.

Jermain Defoe ne ya fara farke wa Sunderland kwallon farko, kuma nan da nan Marc Albrighton ya ci wa Leicester kwallo ta hudu.

Daf da za a tashi daga karawar ne Steven Fletcher ya kara rage kwallon da aka ci Sunderland.