El-Kanemi ta doke Kwara United 1-0

Hakkin mallakar hoto lmc twitter
Image caption Ba a karasa karawa tsakanin Rangers da Shootings ba, sakamakon ruwan sama

Kungiyar El-Kanemi Warriors ta samu nasara a kan Kwara United da ci daya mai ban haushi a gasar Premier Nigeria wasannin mako na 22 da suka yi ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga, Enyimba ta doke Lobi Stars da ci 2-0, fafatawa tsakanin Giwa Fc da Warri Wolves kunnen doki suka tashi, shi ma wasan Dolphins da Abia Warriors 1-1 suka buga.

Kano Pillars karkashin sabon koci Baba Ganaru ta samu maki daya ne a Oghara, a inda ta buka kunnen doki da Bayelsa United, Wikki Tourist da Nasarawa United suka tashi wasan babu ci a tsakaninsu.

FC Taraba kuwa doke Akwa United ta yi da ci daya mai ban haushi, yayin da za a karasa wasan Rangers da Shootins ranar Litinin kuma mintuna 23 da suka rage, an tashi daga wasan ne sakamakon ruwan sama inda Rangers ta ci kwallo daya da nema.

A dai ranar Litinin din za a buga wasa tsakanin FC Ifeanyiubah da Sunshine Stars.

Ga sakamakon wasannin mako na 22 da aka yi:

  • Enyimba 2-0 Lobi Stars
  • FC Taraba 1-0 Akwa United
  • Giwa FC 1-1 Warri Wolves
  • Dolphins 1-1 Abia Warriors
  • El-Kanemi 1-0 Kwara United
  • Wikki Tourists 0-0 Nasarawa United
  • Bayelsa United 1-1 Kano Pillars