An dakatar da alkalan Premier Nigeria uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An gargadi alkalan wasan kwallon kafa na Nigeria da su maida hankali kan aikinsu

Kwamitin alkalai na hukumar kwallon kafar Nigeria ya dakatar da alkalan wasan Premier uku, bayan da aka same su da laifin kasa tabuka abin azo a gani a gasar.

Kwamitin ya yanke wannan hukuncin ne ranar Juma a, bayan da ya yi zama don bitar wasannin gasar kasar wacce aka kammala zangon farko.

Alkalan da aka dakatar sun hada da Alaba Abiodun daga jihar Ogun da Francis Agbaegbu daga Niger da kuma mataimakin alkalin wasa Abubakar Garba Yusuf.

Dukkansu ukun an dakatar da su daga alkalancin wasannin Premier da ake yi har zuwa karshen kakar bana.

Haka kuma hukumar ta ja kunnen Sani Mohammed daga jihar Kaduna da China Blessed daga Rivers da su kara maida hankali wajen gudanar da aikinsu.

Tun a mako na hudu da fara wasannin gasar bana kwamitin ya dakatar da John Charles daga jihar Enugu da kuma O. Matador daga Abia daga yin alkalanci a gasar Premier.'