Ji nake kamar a gida nake tamaula - Ayew

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karon farko da Swansea ta samu maki a Stamford Bridge

Andre Ayew ya ce ji yake kamar a gida yake a Swansea, bayan da ya ci kwallo a karawar farko da ya buga wa kulob din tamaula a fafatawar da suka yi da Chelsea .

Ayew dan kwallon Ghana mai shekaru 25, ya koma Swansea a watan Yuni, daga kungiyar Marseille ta Faransa.

Dan kwallon ya bayar da gudunmawa ga Swansea a wasan Premier da suka yi da Chelsea, a inda ya ci kwallo a karawar da suka tashi 2-2 ranar Lahadi.

Ayew ya ce "Yan wasan Swansea sun ba ni gagarumar gudunmawa, suna kuma taimaka min kan yadda zan fito da kwarewata a tamaula".

Karawar da Swansea ta tashi 2-2 a Stamford Bridge ranar Lahadi ita ce karon farko da kulob din ya samu maki a kan Chelsea.