Arsenal za ta dawo da tagomashinta - Wenger

Image caption Wenger ya ce Arsenal za ta dawo da tagomashinta

Arsenal za ta farfado daga fara gasar Premier bana da kafar hagu, bayan doke ta 2-0 da West Ham ta yi a Emirates in ji Arsene Wenger.

Arsenal ta yi rashin nasara a karawar duk da kaso 62 cikin 100 da ta buga a wasan da kuma kai hari kai tsaye zuwa raga 22 da ta yi.

Wenger ya ce "Watakila 'yan wasa sun taka leda cikin dari-dari, kuma sun sakawa kansu matsin lamba a karawar".

Arsenal wacce ta kammala gasar Premier bara a mataki na uku a kan teburi, na shan matsi daga magoya baya kan ya kamata ta kara sayo sabbin 'yan kwallo a bana.

Kungiyar Arsenal din ta sayo mai tsaron raga Peter Cech daga Chelsea a bana, kan kudi £10m.