Mancity ta doke West Brom da ci 3-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption City ta hada maki uku kenan a wasan farko a Premier

Manchester City ta samu nasara a kan West Brom da ci 3-0 a gasar Premier da suka buga a ranar Litinin.

Yaya Toure ne ya ci kwallon farko a minti na tara da kuma ta biyu a minti na 24 da fara tamaula.

Bayan da aka dawo daga hutu ne kuma kyaftin din City Vincent Kompany ya ci ta uku a minti na 59.

Sabon dan wasan da City ta saya daga Liverpool Raheem Sterling ya buga fafatawar.

A ranar Lahadi City za ta buga wasa na biyu a gasar Premier da Chelsea