An yi watsi da bukatar Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Asmir Begovic ne zai maye gurbin Courtois a wasan

Hukumar FA ta yi watsi da daukaka karar da Chelsea ta shigar kan jan katin da aka bai wa Thibaut Courtois.

Hakan na nufin Courtois ba zai buga karawar da Chelsea za ta yi da Manchester City a gasar Premier ba.

An kori mai tsaron ragar ne daga wasan da Chelsea ta buga 2-2 da Swansea a gasar Premier ranar Lahadi a Stamford Bridge, yayin da ya yi wa Bafetimbi Gomis keta.

Hukumar FA ta ce Chelsea ta gaza bayar da shaidar cewar korar da alkalin wasa Micheal Oliver ya yi wa golan, bisa kuskure ya yi.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho bai ce komai ba kan korar da aka yi wa golan a wasan.

Chelsea wacce ta dauki kofin Premier bara, za ta kara da Manchester City a gasar Premier a Ettihad ranar Lahadi.